DUK RINSTI DUK WUYA BAZAN BAR BEGENKA BAمُـــــحَــــمَّــــدرَّسُـــــولُ اللّٰــــــه ﷺ♥️
TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)
Nasabarsar ta bangaren mahaifinsa: Muhammad(saw) dan Abdullahi, dan Abdul-Mutallib, dan Hashim dan Abdul-Manaf, dan Kusayyi dan Kilabi… nasabarsa(saw) madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Adam(as) a tsatson masu sujadah da tsarki.
Nasabarsa ta bangaren Mahaifiyarsa: Ita ce Aminah ‘yar Wahabi, dan Abdul-Manaf dan Zuhrata dan Kilabi… nasabarsa ta fuskar mahaifinsa da mahaifiyar tahadu wajen Kilab zuwaga Annabi Adam da Hauwa(as).
Wadanda suka reneshi: Abdul-Mulib, Halimah As-Sa’adiyya, da Abu Talib.
Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.
Lakabinsa: Al-amin, Al-mustafah…
Sunayensa da suka zo a cikin Kur’ani mai girma: Khatamin-nabiyyin, Al-ummi, Al-muzzammil, Al-muddassir, An-nazir, Al-mubin, Al-karim, An-nur, Anni’ima, Ar-rahma, Al-abdu, Ar-ra’uf, Ar-rahim, As-shahid, Al-mubasshir, An-nazir, Ad’da’i…
Tarihin haihuwarsa: An haifi Monzon Allah(saw) a Ranar Jumu’ah, 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571 M) (bisa mash’hurin zance daga Ahlul-Bayt(as) (amma a wata ruwayar an haifeshi(saw) ranar Litinin 12 Rabi’u-auwal).
Inda aka haifesa: Makka.
Tambarin zobensa: Muhammadur-Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.
Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.
Aikoshi: An aiko shi a Makka, 27 Rajab; yana dan shekara 40.
Koyarwar sakonsa: ya zo don daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame, sa’annan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah(swt), su kuma Musulmi suka karba daga gare shi.
Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Qur’ani, amma wadanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa; ba zasu kirgu ba, misali, tsagewar wata.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a boye shekara 3, ya kuma kira su a bayyane shekara 10.
Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal, bayan shekara 13 daga aikosa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai; gare shi da kuma Sahabbansa.
Yakokinsa: Allah ya yi wa Manzo(saw) izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar, Uhud, Al-khandak(Ahzab), Khaibar, Hunaini…
Matansa: KHadija ‘yar Khuwailid(as) ita ce matarsa ta farko. Sauran su ne; Saudatu ‘yar Zami’a, A’isha ‘yar Abubakar, Gaziyya ‘yar Dudan(Ummu Sharik), Hafsa yar Umar, Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu Habibia), Ummu Salama ‘yar Abu Umayya, Zainab ‘yar Jahash, Zainab ‘yar Huzaima, Maimuna ‘yar Al-Haris, Juwairiyya ‘yar Al Haris, Safiyya ‘yar Huyayyi dan Akhdab.
‘Ya’yansa: Abdullah, Al-Qasim, Ibrahim, Fatima(as). A wani kaulin akwai Zainab, Ruqayya da Ummu Kulsum.