Sabon majalisin Shehi Ahmad Tajul’izzi a Abuja.

Sabon majalisin Shehi Ahmad Tajul’izzi a Abuja.

Fitaccen mmai yabon Manzon Allah (S.A.W) Shehi Ahmad Tajul’izzi ya sake wani baban majalisi a garin Abuja dake Nijeriya.

GA JERIN WASU HOTUNAN DAGA MAJALISIN

TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Nasabarsar ta bangaren mahaifinsa: Muhammad(saw) dan Abdullahi, dan Abdul-Mutallib, dan Hashim dan Abdul-Manaf, dan Kusayyi dan Kilabi… nasabarsa(saw) madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Adam(as) a tsatson masu sujadah da tsarki.

Nasabarsa ta bangaren Mahaifiyarsa: Ita ce Aminah ‘yar Wahabi, dan Abdul-Manaf dan Zuhrata dan Kilabi… nasabarsa ta fuskar mahaifinsa da mahaifiyar tahadu wajen Kilab zuwaga Annabi Adam da Hauwa(as).

Wadanda suka reneshi: Abdul-Mulib, Halimah As-Sa’adiyya, da Abu Talib.

Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Lakabinsa: Al-amin, Al-mustafah…

Sunayensa da suka zo a cikin Kur’ani mai girma: Khatamin-nabiyyin, Al-ummi, Al-muzzammil, Al-muddassir, An-nazir, Al-mubin, Al-karim, An-nur, Anni’ima, Ar-rahma, Al-abdu, Ar-ra’uf, Ar-rahim, As-shahid, Al-mubasshir, An-nazir, Ad’da’i…

Tarihin haihuwarsa: An haifi Monzon Allah(saw) a Ranar Jumu’ah, 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571 M) (bisa mash’hurin zance daga Ahlul-Bayt(as) (amma a wata ruwayar an haifeshi(saw) ranar Litinin 12 Rabi’u-auwal).

Inda aka haifesa: Makka.

Tambarin zobensa: Muhammadur-Rasulullah!

Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.

Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.

Aikoshi: An aiko shi a Makka, 27 Rajab; yana dan shekara 40.

Koyarwar sakonsa: ya zo don daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame, sa’annan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah(swt), su kuma Musulmi suka karba daga gare shi.

Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Qur’ani, amma wadanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa; ba zasu kirgu ba, misali, tsagewar wata.

Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a boye shekara 3, ya kuma kira su a bayyane shekara 10.

Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal, bayan shekara 13 daga aikosa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai; gare shi da kuma Sahabbansa.

Yakokinsa: Allah ya yi wa Manzo(saw) izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar, Uhud, Al-khandak(Ahzab), Khaibar, Hunaini…

Matansa: KHadija ‘yar Khuwailid(as) ita ce matarsa ta farko. Sauran su ne; Saudatu ‘yar Zami’a, A’isha ‘yar Abubakar, Gaziyya ‘yar Dudan(Ummu Sharik), Hafsa yar Umar, Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu Habibia), Ummu Salama ‘yar Abu Umayya, Zainab ‘yar Jahash, Zainab ‘yar Huzaima, Maimuna ‘yar Al-Haris, Juwairiyya ‘yar Al Haris, Safiyya ‘yar Huyayyi dan Akhdab.

‘Ya’yansa: Abdullah, Al-Qasim, Ibrahim, Fatima(as). A wani kaulin akwai Zainab, Ruqayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa maza: 9 ne, su ‘ya’yan Abdul-Mudallib ne: Al-haris, Zubair, Abu Talib, Hamza, Al-Gaidak, Dirar Al-muqawwam, Abu Lahab da Abbas…

Ammominsa mata: Su 6 ne daga iyaye mata daban- daban sune: Amima, Ummu Hakima, Barra, Atika, Safiyya, Arwa…

Khadiminsa: Anas dan Malik…

Mawakinsa: Hassan dan Sabit, Abdullahi dan Rawahata, Ka’abu dan Malik…

Ladanansa: Bilal Al- Habashi, Abdullahi dan Ummul-Maktum da Sa’ad Al-kirdi.

Tarihin Shahadarsa (wafatinsa): 28 Safar 11 H.

Wajan da ya yi shahada: Madina.

Inda aka binne shi: Madina a dakinsa madaukaki, mai alfarma.

Annabi Muhammad(saw) shine karshen Annabawa(as) kuma addininsa shine Musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari’arsa zata wanzu har zuwa Qiyama kuma ita kadai ce shari’ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa karshen rayuwar Duniya da cigaban rayuwar Lahira.

Annabi Muhammad(saw) abin koyi ne ga dukkan Duniya baki daya, dukkan mutanen duniya idan suna son alkhairi ga kawukansu; to dole ne su bi tarfarkinsa(saw); su yi koyi da kyawawan halyensa(saw) da kuma sanin tarihinsa da siffofinsa(saw):

Annabi Muhammad(saw) dan Abdullah da Amina, an haife shi a Makka ranar juma’a goma sha bakwai ga watan Rabi’ul-awwal, bayan bullowar Al-fijir a shekarar giwa…

An aiko Annabi Muhammad(saw) da sako a 27 ga Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibril(as) ya sauka gareshi daga wurin Allah(swt) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaq. Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokacin akwai jama’a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi; yana cewa da su: “Ku ce babu abin bauta sai Allah ku rabauta”. A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka rika yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk lokacin ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce; “Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni”.

jihadi…

Jikinsa(saw) ya kasance kololuwa wajen kyau, daidaito, dacewa… kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye, ladabi, dabi’a… sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.

Atakaice; Annabi(saw) ya tattara dukkan wata dabi’a mai kyau, girma, daukakada, ilimi, adalci, takawa, iya tafiyar da al’amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.

Wannan shine Annabin musulmi kuma wannan shine addinin Musulunci, addininsa(saw) shine mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai, domin shi: “Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo”.

By wasiyya

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Danna Ka Samu Sabon Tallafin ₦50,000