Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin jinjirin Watan Ramadan a Najeriya.
A wani jawabi da ya gabatar, Sarkin Musulmin ya ce an ga jinjirin watan na Ramadana a daren Litinin, inda ya ce Litinin din 11 ga watan March 2024 ce ranar karshe ta watan Sha’aban na Shekarar Hijira ta 1445.
Sannan ya ce Litinin 11 ga watan March 2024 ce ranar farko ta watan Ramadana na Shekarar Hijira ta 1445.
“Ƴan uwa al’ummar Musulmi, bisa ga sharuddan Musulunci, muna sanar da ku cewa yau Lahadi 29 ga watan Sha’aban shekara ta 1445 bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 10 ga watan Afrilun shekarar 2024, an kawo karshen watan Sha’aban na shekara ta 1445,” in ji Sarkin Musulmi.
“Mun samu tabbacin ganin Watan Ramadan daga kungiyoyi da shugabannin Musulmi daga koina a cikin kasar nan, kwamitocin tantance ganin wata na kasa da na jihohi sun tantance kuma mun tabbatar.”
Sarkin Musulmi ya kuma shawarci jama’a da su kiyaye dokokin da aka kafa na annobar korona, tabbatar da ba da tazara da kuma sanya takunkumi yayin sallolin dare.
Ya roki al’ummar Musulmi da su yi wa Najeriya addu’a yayin azumin kan matsalar tsaro da ta a’ddabi kasar baki daya.
Sultan Sa’ad Abubakar III ya roki masu arziki da su rika taimakawa marasa karfi domin tabbatar da soyayya da kaunar juna.
Kamar Najeriya, haka ma kasashen Musulmai da dama, da suka hada da Saudiyya sun sanar da ganin Watan Ramadana din a ranar Litinin