Innalillahi; Abun da yayi sanadiyyar mutuwar jaruma Saratu Giɗaɗo Daso shine…

Innalillahi; Abun da yayi sanadiyyar mutuwar Hajiya Saratu Giɗaɗo Daso shine…

Allah yayiwa fitacciyar jarumar fina-finan hausa Saratu Gidado Daso rasuwa za,ayi, jana’izarta da karfe 4:30 na yamma a Jihar Kano.

Alhassan Kwalli wanda shi ne shugaban jarumai na Kannywood ya shaida wa BBC cewa marigayiyar ta yi rasuwar fuju’a ne bayan ta yi sahur na azumin karshe na yau Talata.

“Tana zaune da iyalanta sai ta fada wa mutane cewa kowa ya je ya kwanta domin a ci gaba da ibada domin neman yardar Allah. To amma da safe ba a ga fitowarta ba har zuwa karfe daya na ranar nan ta Talata, to shi ne ‘yan uwanta suka yi ta kwankwasa kofar har ta kai ga an balle kofar, inda kuma aka gan ta rai ya yi halinsa.” In ji Alhassan Kwalli.

Alhassan ya kuma shaida wa BBC cewa za a yi jana’izar fitacciyar jarumar da misalin karfe huɗu na yamma, bayan yin gwaje-gwaje a asibiti.

A zantawa da wakilin mu Shuaibu Abdullahi ta wayar tarho, wani Dan jarida a Jihar Kano ya ce lafiyar ta kalau ta kwanta bacci ne kawai daga can Rai yayi halin sa.

By wasiyya

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Danna Ka Samu Sabon Tallafin ₦50,000