CIGIYA: Bilkisu ‘yar Kimanin Shekara 23 Daga Fita Sallar Turawihi A Daren Talata Har Yanzu Babu Labarinta

CIGIYA: Daga Fita Sallar Turawihi A Daren Talata Har Yanzu Babu Labarinta

Muna cigiyar wannan matashiya mai suna Balkisu Adamu Muhammad, wacce aka fi sani da [Sabeera] ta bace a daren ranar Talata 19 ga watan maris na shekarar 2024.

Ta bace ne a daidai lokacin data fita sallar tarawihi a rukunin gidajen ma’aikatan kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Bauchi.

Bilkisu ‘yar kimanin shekaru 23 ne sannan fara ce, don haka ne muke rokon duk wanda Allah Ya sa ya ji labarin ta da yakai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ya ‘kira wannan lambar waya 0803 621 7196.

Don Allah ku yada (sharing) ko Allah zai sa a dace.

Ya Allah ka bayyana ta cikin aminci.

Sanarwa daga
Usman Ibrahim Kobie
|21|MARCH|2024|

By wasiyya

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Danna Ka Samu Sabon Tallafin ₦50,000