An gurfanar da jarumar Kannywood Amal Umar a gaban Kotu bisa zargin bawa ƴan sanda cin hanci bayan kama ta da lefi

An gurfanar da jarumar Kannywood Amal Umar a gaban Kotu bisa zargin bawa ƴan sanda cin hanci bayan kama ta da lefi.

‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Jarumar Kannywood Amal Umar A Gaban Kotu

Rundunar ‘yan sanda shiyya ta ɗaya Zone One, dake jihar Kano, ƙarƙashin AIG Umar Mamman Sanda, sun gurfanar da guda daga cikin ‘yan masa’antar shirye fina-finan Hausa ta Kannywood, mai suna Amal Umar, a gaban kotun majistiri mai lamba 24, dake zamanta a unguwar Gyadi-Gyadi.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan shiyya ta ɗaya CSP Bashir Muhammad ya fitar, aka aikawa manema labarai.

An dai gurfanar da Amal Umar ne a gaban kotun bisa zargin ta da yunƙurin bada cin hancin Naira dubu ɗari biyu da hamsin (250,000), ga ɗan sandan da ke bincike a kan wani laifi da ake zargin da hannun ta wajan aikata wa.

By wasiyya

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Danna Ka Samu Sabon Tallafin ₦50,000